Lauyoyin Zuman sun bukaci a jinkirta domin ya samu damar bayyana da kansa,ya kuma gana da su sosai.
Ana zargin Zuma da cin hanci ta hanyoyi daban-daban, da zamba a wani gagarumin cinikin makamai da aka yi cikin shekarar 1999 da gagarumin kamfanin kayayayakin tsaro na Faransa mai suna Thales, lokacin yana mataimakin shugaban kasar ta Afrika ta Kudu.
Shi ma kamfanin ana tuhumarsa da cin hanci da kuma laifin badda sawun-kudi.
Zuma Dan shakara 79 a Duniya ya bayyana ne a ranar litinin da ta gabata ta kafar faifan bidiyo daga gidan gyaran halin da yake zaman kaso na wattani 15, wanda kotun tsarin mulki ta yanke ma sa a cikin watan Yuni, a sakamakon kin bayyana da kansa gaban kotun kan zarge-zargen cin hanci, yayin mulkinsa na shekara tara, wanda ya kare a shekara 2018.