Tawaggar ta ECOWAS ta kuma kunshi shugabar kasar Liberia, Ellen Johnson Sirleaf, wacce itace ma shugabar ECOWAS din, da shugaba Earnest Bai Koroma na Saliyo da kuma tsohon shugaban Ghana, John Dramani Mahama.
Wannan balaguron nasu zuwa Banjul ci gaba ne da kokarin da suke na warware rikicin siyasar kasar da ya biyo bayan zaben da aka yi a cikin watan Disamba wanda kuma shi Adama Barrow ya lashe, kuma yanzu haka yake ci gaba kimtsawa don daukan rantsuwar kama aiki a ran 19 ga watan nan na Janairu duk kuwa da kalaman da shi shugaba mai barin gado Yahya Jammeh yayi kwanan nan na cewa shi zai ci gaba da zamansa kan kujerar har sai ranarda Kotun Koli ta kasar tashi ta yanke hukunci akan karar da ya shigar, yana kalubalantar zaben.
Sai dai abinda ba tabbas a kansa shine ko idan shugabannin kasashen na Afrika zasuyi nasarar cusawa shi Jammeh ra’ayin ya hakura ya sauka tun kafin ranar rantsarda Adama Barrow ta zo.
Yayinda wannan ke faruwa ne kuma Majalisar Dokokin Nigeria ta jefa kuri’ar amincewa da cewa a yi wa shi shugaba Jammeh tayin yazo a bashi mafakar siyasa a Nigeria don a karfafa mishi gwiwar sauka cikin lumana.