Da farko shugaba Yahya Jammeh ya amince da shan kaye kuma har ma ya taya Adama Barrow murna, amma daga bisani sai ya janye amincewar tasa a ranar Juma’a da ta gabata inda yayi korafi gameda kurakurai da yace jami’an zabe sun yi.
Kira da jami’iya mai mulkin ta yi ga Kotun kolin ya zo ne daidai lokacin da tawagar shugabannin kasashen Afrika ta Yamma suka isa kasar ta Gambia don ba shugaba Jammeh shawara da ya amince da sakamakon zaben bayan ya kwashe shekaru sama da ashirin da biyu yana mulkin kasar.
Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya shaidawa kampanin dillacin labarai na Reuters cewar shugaba Jammeh ya yiwa tawagar tasu tarbo mai kyau.
Tun tuni ne dai jami’an tsaro suka shiga ofishin hukumar zaben kasar kuma suka umurci shugaban hukumar da ya bar ofishinsa, kuma sun killace ginin, sun hana kowa shiga wurin.