Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Hukumar Zaben Gambia Ya Arce daga Kasar


Yahya Jammeh shugaban Gambia da ya sha kaye amma yaki ya amince ya mika mulki
Yahya Jammeh shugaban Gambia da ya sha kaye amma yaki ya amince ya mika mulki

Shugaban hukumar zaben kasar Gambia yayi ta kare domin ko ya rce daga kasar bayan da ya samu sakon barazanar da ake yiwa rayuwar sa, bayan ya bayyana shugaba Yahaya Jameh a matsayin wanda ya fadi zaben da aka yi a cikin watan jiya.

Kamar yadda ‘yan uwan shugaban hukumar zaben Alieu Mamar Njai, suka ce yanzu haka ya gudu zuwa kasar Senegal bayan ya samu labarin cewa mahukuntar kasar ta Gambia na kulla wata makarkashiya gameda shi.

Haka kuma wata sabuwa,kanfanin dillacin labarai na Reuters tace babban hafsan sojan kasar ta Gambia ya jaddada goyon bayan sa ga shugaba Yahaya Jameh.

Wannan batu ya fito fili domin ko Janar Ousman Badjie ya rubuta wa shugaba Yahaya Jameh wasikar nuna goyon bayan sa kuma an buga wannan wasikar a jiya, cikin wata jaridar da ke goyon bayan gwamnatin kasar.

Jammeh dai ya kwashe shekaru 22 yana mulkin ‘yar karamar kasar ta Gambia, wanda saia farkon watan Disambar shekararda ta wuce ne aka bayyana shi a matsayin wanda ya fadi a zaben da akayi.

Da farko ya karbi shan kaye, amma kuma daga bisani sai jam’iyyar sa ta kai maganar kotu tana zargin wai an tafka magudi lokacin zaben.

Yanzu dai a ranar 10 ga wannan watan ne ake sa ran babban kotun kasar ta yanke hukunci game da wannan batu.

To sai dai duk da wannan kiki-kakan da ake ciki zababben shugaban Adama Barrow yace zaici gaba da shirye-shiryen bikin rantsarda shi a matsayin sabon shugaban kasar ta Gambia a ranar 19 ga wannan wata.

Yanzu haka dai MDD da sauran wasu kasashen Africa sun bukaci Jammeh da ya sauka daga kan karagar mulkin cikin ruwan sanyi.

XS
SM
MD
LG