Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yahya Jammeh Na Gambia Yace Allah Ne Kadai Zai Hanashi Nasara


Yahya Jammeh da mayarsa Zineb Jammeh
Yahya Jammeh da mayarsa Zineb Jammeh

Shugaban kasar Gambia da ya dade a kan karagar mulki Yahaya Jammeh yace Allah kadai zai hana masa nasara a kokari da yake yi na murda sakamakon zaben shuagaban da kasar tayi a cikin wannan wata.

Zababben shugaban kasar Adama Barrow ya doke shugaba Jammeh a zaben na ranar daya ga wannan watan. Da farko shugaba Jammeh ya amince da sakamakon zaben amma yanzu ya yi burus yanazargin cewa akwai kura kuarai a zaben don haka yake so kotun kolin kasar ta soke sakamakon.

Yace baya tsoron kowa a wannan duniya inji shugaba Jammeh a wani jawabinsa ta telbijin ga kasar. Yace yana son ya ga an tabbatar da adalci. Yace shi mutum ne mai son zaman lafiya amma ba matsoraci ba.

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar tarayyar Afrika ta AU da kungiyar ECOWAS dukkaninsu sun gargadi shugaba Jammeh da ya amince da shan kaye kuma ya mika mulki ga Barrow.

Shugaban ya caccaki sauran shugabannin kasashen Afrika ta Yamma da suke kira da ya sauka daga mulki, yace basu da hurumin nuna masa abin da zai yi.

Kotun kolen kasar ta ajiye ranar 10 ga watan Janairu ran da saurari kara da Yahaya Jammeh ya kai matakwanaki tara kafin ya mika mulki.

XS
SM
MD
LG