Hukumar da ke yaki da yaduwar cututtuka ta NCDC a Najeriya ta ce yawan mutante da suka mutu sanadiyyar annobar COVID-19 ya karu da mutum uku.
NCDC ta bayyana hakan ne a shafinta na yanar gizo inda ta ce a ranar Juma’a mutum uku suka rasu, hakan ya kai adadin zuwa 2,181.
Mutanen kuma da ke fama da cutar a yanzu haka sun kai 9, 542 yayin da jimullar mutanen da cutar ta harba ya kai 177, 142.
“A ranar 6 ga watan Agustan 2021, mutum 565 aka tabbatar sun kamu da cutar kana 3 suka mutu a Najeriya.”
A cewar hukumar, an gano sabbin wadanda suka kamu da cutar ne a jihohi 17.
“Legas 348, Rivers 70, Akwa Ibom 40, Oyo 36, Abuja 24, Ekiti 15, Kwara 7, Ogun 7, Gombe 3, Anambra 2, Kaduna 2, Bayelsa 1, Cross River 1, Edo 1, Filato 1, Kano 1 da kuma Sokoto 1.” In ji hukumar ta NCDC.