Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Gabas Ta Tsakiya Ka Iya Shafar Najeriya - Masana


Rikicin Gabas-ta-tsakiya
Rikicin Gabas-ta-tsakiya

Ganin cewa rikicin na gabas ta tsakiya sai ƙara rincaɓewa yake yi, masana a Najeriya sun yi kira ga shugabanin Afirka da su yi azama wajen ganin cewa an kawo ƙarshen rikicin ba da daɗewa ba.

Rikici tsakanin Falasdinu da Isra'ila ba sabon abu ba ne a yankin Gabas-ta-Tsakiya. Sai dai irin wannan arangama da luguden wuta da ke faruwa a yanzu haka tsakaninsu, rikici ne da ya ɗauki hankalin ƙasashen duniya.

Idan aka duba ƙasashen dake yankin Gabas-ta-Tsakiya, wasu sun haɗa iyakoki da ƙasashen Afirka, wanda hakan ya sa wasu 'ƴan Afirka ke fatan a kawo ƙarshen wannan rikici ba da ɗaɗewa ba.

Wasu manazarta na ganin cewa ya kamata Najeriya ta fuskanci wannan rikicin da ke tsakanin kungiyar Hamas da ƙasar Isra'ila, ganin cewa ita ce yaya babba a nahiyar Afirka.

Ambassada Hassan Arɗo Jika, tsohon Jakadan Najeriya ne a ƙasar Trinidad and Tobago, ya ce "wannan rikici zai shafi Najeriya tunda ita ce babba a nahiyar Afirka, dan haka dole ne Najeriya ta saka baki wajen ganin al'amura sun dawo dai-dai a yankin Gabas-ta-Tsakiya".

A hirarsa da Muryar Amurka, Farfesa Ibrahim Umara Gudunbali na Jami'ar Tarayya da ke Maiduguri, ya shaida cewa "wannan rikici da ke faruwa yanzu haka tsakanin Falastinu da Isra'ila zai shafi harkar tsaron Najeriya da ma Afrika baki-ɗaya idan ba'a yi taka-tsan-tsan ba, saboda nahiyar ta haɗa mabambantan addinai, kuma wasu na ganin wannan rikici, kamar rikici ne na addini, wanda kuma ba haka ba ne".

Nasiru Marmara, manazarci kan harkokin tattalin arziki da ci gaban ƙasashe, ya shaida wa Muryar Amurka cewa, "wannan yamutsi da ke faruwa yanzu haka tsakanin Falasdinu da Isra'ila, zai shafi tattalin arzikin Najeriya da ma nahiyar Afirka, saboda akwai alaƙar kasuwanci mai karfi tsakanin ƙasashen na Gabas-ta-Tsakiya da Najeriya".

Saurari rahoton Ruƙaiya Basha:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:46 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG