Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Isra'ila Da Hamas Na Iya Shafar Kudaden Shigar Najeriya Ta Fannin Man Fetur - Kwararru 


Tallafin Mai A Najeriya Ya Haura Dala Biliyan 1 A Watan Agusta Yayin Da Take Kara Samar Da Man Fetur
Tallafin Mai A Najeriya Ya Haura Dala Biliyan 1 A Watan Agusta Yayin Da Take Kara Samar Da Man Fetur

Masana sun bayyana cewa rikicin Isra’ila da Hamas ka iya sa ‘yan Najeriya fuskantar kalubale  wajen sayen man fetur duk da cewa an sami hauhawar farashin man fetur a duniya, lamarin da ya kamata a ce ya taimaka wa masana’antar danyen mai ta kasar. 

Karuwar farashin mai a duniya zai kawo ƙarin kudaden shiga daga sayar da danyen mai, in ji masanan, amma sai dai kuma a lokaci guda karancin matatun mai a Najeriya zai haifar da tsadar mai ga masu saye.

Gabas ta tsakiya ita ce ke da kusan kashi daya bisa uku na yawan man da ake sarrafawa a duniya.

Emmanuel Afimia, wanda ya kafa kamfanin Enermics da ke Legas, ya ce ’yan Najeriya za su ji radadin duk wani karin farashin mai saboda a kwanakin baya gwamnati ta dakatar da biyan tallafin man fetur.

Karancin man fetur a Najeriya.
Karancin man fetur a Najeriya.

"Idan aka samu cikas wajen samar da man, lamarin zai shafi ‘yan Najeriya a cikin gida saboda… an cire tallafin mai, kuma yanayin kasuwa ke tantance farashin man fetur," in ji Afimia.

"Najeriya na bukatar ta shirya don yuwuwar hauhawar farashin man fetur a cikin gida," in ji Afimia.

Duk da cewa Isra'ila da Falasdinu ba su ne manyan kasashen da ke samar da mai ba, farashin mai a duniya ya karu da kashi 4% a ranar Litinin – alamar da ke nuna cewa farashin na iya kara hauhawa, in ji masana.

A rubuce, karin farashin man fetur ka iya amfanar Najeriya, daya daga cikin kasashen da ke kan gaba wajen samar da danyen mai a Afirka.

Sai dai kuma Najeriya ba ta tace danyen mai a cikin gida, ta na dogara ne ga shigo da shi daga kasashen waje domin biyan bukatunta, in ji Afimia.

Watanni da suka gabata hukumomin Najeriya sun ba ‘yan kasuwar man fetur masu zaman kansu damar shigo da mai. Wannan na zaman daya daga cikin sauye-sauyen tattalin arziki da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi na yaye ‘yan Najeriya daga tallafin man fetur.

Sai dai a ranar Litinin, kamfanin man Najeriya na NNPC, ya ce rashin kudin kasashen waje na kawo cikas ga dillalan mai masu zaman kansu, don haka NNPC ce kadai ke shigo da mai.

Chukwudi Odoeme, wanda ya kafa Obiama Africa Network for Development, wata kungiya mai zaman kanta da ke jan hankali kan damuwar ‘yan kasa, ya ce “Abin da ke faruwa shi ne ‘yan kasar za su kara fuskantar matsin rayuwa.”

A watan Agusta, hukumomin Najeriya sun yi alkawarin sake farfado da matatun mai na jihohi hudu nan da karshen shekarar 2024.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG