Ganin yadda a ‘yan kwanakin nan ‘yan kungiyar Boko Haram, ke kai hare haren kunar baki wake wani masanin dabarun tsaro Malam Daladi Abdu, yace jama’a lura da bakon fuska, da kuma yin la’akari da irin sitira da suke sanye da ita zai tamaka wajen ganesu a cikin jama'a.
Domin a cewar sa irin sitirar da ‘yan kungiyar masu nufi aikata aika aika ya sha banban da irin sitiran mutanen wajen da suke son yinwa tu’annati, ta yadda yake zasu sa sitira ne mai yalwa mai fadi ko mai girma domin kada aga abunda suke dauke dashi wa lau Bom din da suke dauke dashi sun daure shi a jikinsu ne ko kuwa suna dauke dashi a wani muzibi ne jaka ne ko akwati ko abunda yayi kama da wannan haka suke yi wajen sa sitira kennan.
Sanan baya ga haka su mutane nen wadanda yake yayin da suka fuskacin abunda suke so suyi ma’ana wuri da suke so su tada Bom dinsu babu wani abunda yake dauke masu hankali akan wannan wato abunda suke kallo kawai inda suka tunkara, basu yin waige ko kayi Magana dasu ba zasu amsa bat oh idan aka ga mutane masu irin wadannan daya daga cikin alamu ne da za’a gane su.
Sai kuma yanayi na fuska saboda mutumin da yayi niyyar aikata irin wannan mugun abu zaka ga fuskan shiyana cikin takura da damuwa ta yadda za’a ga jijiyar fuska ta fito da kuma baki na motsi.
Duk da irin wadannan matsaloli rudunar Sojojin Najeriya, na cewa nan bada dadewa ba za’a kawo karshen matsalar Boko Haram.