'Yan sandan jihar Adamawa sunce ana ci gaba da binciken dalilin rasuwar mataimakin gwamnan jihar Borno Alhaji Zannah Umar Mustapha.
Mataimakin gwamnan ya rasu ne a otel din daya sauka kwanaki a lokacinda ya kai ziyara birnin Yola jihar Adamawa arewa maso gabashin Nigeria.
Duk kokarin da wakilin sashen Hausa yayi na jin ta bakin shugabanin asibitin SMC inda aka gawar yaci tura. Shugaban asibitin Professor Awwal Abubakar yace basu da izinin baiyana sakamakon bincikensu sai da yarda ko kuma amincewar iyalin mamaci.
Dr Bala Saidu na Asibitin kwararu dake jihar Adamawa yace ana binciken mamace a gane dalilin mutuwarsa. Au an harbe shi ne, ko an zuba masa guba a cikin abinci ne ko kuma jini ne ya fashe a cikinsa, sune dalilan daya sa dole a gane, kuma ana iya ganewa.
Wasu basu goyi bayan a bincike gawar ba, wasu kuma sun goyi bayan a bincike gawa, idan ana zaton da walaki goro a miya.