Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abin Da Masana Ke Cewa Kan Zaben Shugabanni Da APC Ta Yi A Kananan Hukumomi


Wani taron jam'iyyar APC da aka yi a jihar Cross River (Facebook/ Benedict Ayade).
Wani taron jam'iyyar APC da aka yi a jihar Cross River (Facebook/ Benedict Ayade).

A Najeriya, a daidai lokacin da ake zargin jam'iyar APC mai mulkin kasar da shure umurnin kotu ta gudanar da zabukan shugabanninta a matakin kananan hukumomi, hakan ya sa masana suke ci gaba da bayyana ra'ayoyi mabanbanta.

Ba sabon batu bane samun baraka tsakanin magoya bayan jam'iyun siyasa idan suka gudanar da zabuka har dai in an saba dokoki ko ka'idojin jam'iya.

To sai dai masana kimiyar siyasa na ganin ya kamata a ce dimokradiyar Najeriya ta wuce irin wannan matakin na samun baraka sanadiyar zabe, domin shekaru sama da ashirin da ta yi ta isa tashi daga zama jaririyar dimokradiya.

Zabukan da jam'iyar APC ta gudanar kwanan nan dama na makonnin baya sun bar baya da kura a wasu jihohi domin korafe-korafe suna son ruruta wutar husuma tsakanin ‘ya'yanta kamar abin da ke faruwa a Sokoto inda aka yi zabe biyu na bangarori biyu a jam'iya daya.

Honourable Abdullahi Balarabe Salame dan majalisar wakilai ne kuma yana cikin masu fafatuka a dayan bangaren, ya ce shugabannin ba su gudanar da zabukan akan ka’ida ba, amma su sun gudanar da zaben yadda ya kamata dalilin da ya sa aka gudanar da zabe biyu.

Shi kuwa shugaban riko na jam'iyar na jaha Isa Sadiq Achida yace ba haka lamarin yake, don ba su suka gudanar da zabe ba.

To ko yaya masana ke kallon wannan dambarwa? a ganin Farfesa Tanko Yahaya Baba, ‘yan siyasa ba su damu da harkokin rayuwar jama’a ba.

Masana dai na cike da mamakin ganin yadda har yanzu ‘yan siyasar Najeriya ke yawo da hankulan jama'a maimakon a hada kai a yi wa talaka aiki.

Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir:

Abin Da Masana Ke Cewa Kan Zaben Shugabanni Da APC Ta Yi A Kananan Hukumomi
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG