Hukumar zabe tace shugaba Edgar Lungu na jami’iyar Patriotic Front mai mulkin kasar ya samu sama da kashi hamsin na kuru’un da aka kada, a yayind da abokin karawansa Hakainde Hichilema na United Party for National Development (UPND) ya samu kashi 48 na kuriu’n.
Shugaban hukumar zaben Easu Chulu ya ayyana shugaba Lungua matsayin zababben shugaba bayan ya bayyana sakamakon zaben na ranar Alhamis.
Sai dai kuma kusoshin jami’iyar adawan sunyi zargin cewa an tafka magudi a zaben, don haka zasu kai kara ga kotun Tsarin Mulki ta Zambia.
Mataimakin kakakin jami’iayar adawa ta UPND kuma wakilin majalisa Cornelius Mweetwa yace fashi ne kawai aka yi musu a wannan zaben, aka murda abinda jama’a suka zaba.” Shima wani lauya na ‘yan adawa, ya tabbatarda da cewa suna da shedar da zata nuna magudin da aka yi a zaben.
To amma wata wakiliyar jam’iyyar da tayi nasara, Mubi Phiri, ta nuna cewa fasalin yankuna da tsarin al’ummar kasar zasu nuna cewa zargin magudi da ‘yan jam’iyyar UPND ke yi bashi da hujja.