Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Zambia ya kira jami'an tsaro su maido da doka da oda cikin gaggawa


Shugaban Zambia Edgar Lungu
Shugaban Zambia Edgar Lungu

Umurnin na shugaba Edgar Lungu ya biyo bayan jita-jitar da ake yadawa wai wasu suna kishe mutane suna tsafi da wasu sassan jikinsu domin habaka tattalin arzikinsu lamarin da ya kaiga tashin hankali da kone-kone a wasu biranen kasar.

Gwamnatin Zambia tace zanga-zanga da kashe kashen da ake yi sun biyo bayan jita-jitar da ake ta yadawa cewa wasu baki mazauna kasar ne suke kashe mutane suna tsafi dasu domin habbaka lamuran kasuwancinu da tattalin arziki.

Jita-jitar ta harzuka matasan kasar wadanda suka farma baki dake kasar suna lalata wuraren da suke sana'a tare da kone gidajensu da kuma raunata wasu. Matasan sun zargi bakin da yin tsafi da mutane domin habaka kasuwancinsu tare da tara dimbin arziki. Matasan sun yashe shaguna da dama

Ministan ma'aikatar yada labarai na kasar Zambia Chishimba Kambwili yace ana iya sassauta dokar ta shugaban kasa idan an samu kwanciyar hankali nan da zuwa gobe Alhamis saboda an soma samun daidaito a wasu garuruwan. Idan hakan ya cigaba Shugaba Edgar Lungu zai sassauta dokar.

Lamuran da suka faru cikin kwanaki hudu da suka gabata ba'a taba ganin irinsu ba a kasar Zambia, inji ministan yada labaran. Yace haka kurum aka soma yada jita-jita cewa baki dake kasuwanci a kasar suna kashe mutane suna tsafi dasu domin su inganta kasuwancinsu. Saboda haka wasu bata gari suka yi anfani da wannan damar suka soma wawure shagunan mutane suna yiwa rayuwarsu barazana. Yace sun yi anfani da 'yansanda amma abun ya gagara.

Dalili ke nan da shugaban kasar ya dauki tsauraran matakai domin kada a jefa kasar cikin wani halin da zai fi karfin kowa, inji minista Kambwili. Yace idan sun bar masu saka jari a kasar, 'yan kasa da baki, takardar kudin kasar kwacha ka iya faduwa kasa warwas lamarin da zai gurfanar da tattalin arzikin Zambia.

Kawo yanzu 'yansandan kasar sun samu nasarar cafke gungun wadanda suka haddasa tashin hankalin da kuma suka fasa shagunan mutane.

Amma wasu 'yan kasar suna zargin 'yan siyasa da hannu cikin lamarin domin wai wasunsu sun yi anfani da rikicin suka kai ramuwar gayya kan 'yan hamayyarsu. Minista Kambwili yace tana yiwuwa wasu 'yan siyasa sun yi anfani da tashin hankalin su kai hari kan 'yan hamayyarsu amma sai an tabatar da hakan tukunna.

'Yansandan kasar sun kama mutan 249 wadanda suka zarga da haddasa tashin hankali da wawure dukiyar mutane. Baicin wadannan 'yansandan sun sake kama wasu 11 dake taimaka masu wurin binciken zargin yin tsafi da mutane lamarin da ya kaiga aika-aikar.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG