Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Kada Kuri’a Na Dokin Yin Zabe a Angola


Shugaban Angola Jose Eduardo dos Santos da ke shirin barin mukaminsa a karon farko tun bayan da ya hau mulki a 1979
Shugaban Angola Jose Eduardo dos Santos da ke shirin barin mukaminsa a karon farko tun bayan da ya hau mulki a 1979

A karon farko cikin gwamman shekaru, al'umar kasar Angola za su shiga rumfunan zabe domin kada kuri'unsu a zaben shugaban kasar da za a yi ba tare da shugaban kasar ba.

Kasar Angola na shirin gudanar da zaben shugaban kasa mai cike da tarihi, yayin da shugaba Jose Eduardo Dos Santos, ke shirin kaucewa gefe bayan da ya kwashe shekaru 38 yana mulkar kasar.

Kashi biyu cikin uku na al’umar kasar ta Angola, ba su san wani shugaba ba illa Dos Santos, yayin da mafi aksarin wadanda suka cancanci su kada kuri’a, ba su taba ganin kuri’a babu sunansa akai ba.

Shi ya da yawa daga cikin al’umar kasar musamman masu kada kuri’ar, da yawansu ya kai miliyan tara, na shaukin zaben ne saboda za su kada kuri’a a karon farko ba tare da sunan shugaban a kan kuri’ar ba.

Wani rukunin masu zaben da shi ma ke cike da shauki, shi ne rukunin matasan da za su kada kuri’a, wadanda shugaba Dos Santos ya yi ta mulki tun daga aka haife su.

Sai dai wani batu da ya fi jan hankulan kowa a daidai lokacin shi ne yadda ake fama da rahsin ayyukan yi, wanda batu ne da jam’iyya mai mulki da mai hamayya suka sha alwashin magancewa idan aka zabe su.

A dai ranar Laraba mai zuwa al’umar kasar za ta kada kuri’ar zaben sabon shugaban kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG