COLOGNE, GERMANY - Ministan Ilimi na Faransa Gabriel Attal a yayin da yake jawabi kan muhimmancin ilimin boko da kuma irin kalubalen da ya ce makarantun Faransa ke fuskanta a watannin da suka gabata, na cin zarafi mai nasaba da addini da ya karu a kasar ne ya bayyana haka.
Batun na hana sanya abaya ko Hijabi, da aka jima ana tafka muhawara mai zafi a tsakanin masu goyon bayan hana dalibai zuwa makaranta da Abayan da kuma masu adawa da dokar da ke ganin wani shiri ne na takurawa Musulmai mata da ke sanya Abaya a kasar ya ci gaba da daukar hankali a ciki dama wajen kasar.
Amma Muryar Amurka ta ji ta ta bakin wasu mata da dokar ta shafa kamar Halima Sanda, Musulma wacce ita kira tayi kan a tattauna domin samar da maslaha ga kowane bangare da baton ya shafa.
Halima ta ce ‘’a game da wannan matakin dai, ni musulma ce kuma na san Faransa ba ta son al’amrin da ke nuna alamar addinin da mutum ya ke bi, amma abin da ya dace, a nemi mafita ta hanyar tattaunawa a cimma matsaya na bai wa mata Musulmai damar sanya duk wani abu na rufe gashinsu ba tare da sai lallai sun yi amfani da Abaya ba’’
Rahotanni dai na nuni da cewa, akwai Musulmai fiye da miliyan biyar da ke rayuwa a Faransa amma batun hana sanya Hijabi ko Abaya batu ne da aka jima ana kai ruwa rana a kai a tsakanin gwamnatin da Musulmin da ke sanya tufafin a daidai lokacin da ake samun karuwar daliban da ke sanya abaya a kasar.
Dakta Garba Moussa mai sharhi kan siyasar kasa da kasa a Faransa ya ce yanzu dai abin da ya rage a wannan yanayi shine kungiyar Musulmai a Faransan ce za ta dauki mataki na gaba don kalubalantar dokar a gaban shari’a.
Tun dai daga shekarar 2004 Faransa ta ayyana dokar da ta haramta amfani da kallabi koma rufe gashin kai a duk makarantun gwamnati da ke kasar, abin jira a gani shi ne ko matakin zat yi tasiri a kokarin Gwamnatin Faransan na raba addini da al’amuran rayuwa ko a'a
Da kuma sakamakon da ake ganin zai iya biyo bayan matakin da Musulmai na Faransa za su dauka na neman kare ‘yancinsu da zarar dokar ta soma aiki a watan Satumba mai zuwa
Saurari cikakken rahoto daga Ramatu Garba Baba:
Dandalin Mu Tattauna