Tun bayan mutuwar matashiya Mahsa Amini ‘yar shekaru 22 a watan Satumba a hannun 'yan sandan da'a na Iran, wadda aka kama a kan laifin saba dokar sanya kaya bisa ga tsarin addinin Musulunci, aka barke da gagarumar zanga-zanga a fadin kasar. Dubban mutane a karkashin jagorancin mata tare da mazajensu, da ’ya’yansu maza, da kannensu maza, da kuma abokan hulda, suka fito kan tituna saboda mutuwar Amini da kuma umurnin cewa dole mata su sanya hijabi don rufe gashin kansu da kuma jikinsu. Zanga-zangar da aka yi ta neman a mutunta “Mata! Rayuwarsu! da 'Yancinsu!" ta rikide ta koma zanga-zangar nuna adawa da cin hanci da rashawa, da danniya da gwamnatin ke yi. Wannan shi ne kalubale mafi girma da gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fuskanta tun bayan kafuwarta a shekarar 1979.
Shugabannin Iran sun mayar da martani ta hanyar dakatar da 'yan sandan da'a daga yin sintiri a kan titi na wani dan lokaci, haka kuma sun mayar da martani, ta hanyar murkushe masu zanga-zangar: an kashe mutane 500; An kama wasu 20,000; kuma an yanke wa wasu akalla 7 hukuncin kisa.
Yanzu, watanni biyu kafin zagayowar ranar da aka kama Mahsa Amini, hukumomin ‘yan sanda sun ba da sanarwar cewa “ba tare da bata lokaci ba,” za su soma yin sintiri a kan tituna don fara gargadi, daga nan su kama matan da suka ci gaba da karya dokar sanya tufafi. Sanarwar na zuwa ne bayan matakin da hukumomi suka dauka a farkon wannan shekarar na rufe masana’antun da suka zarga da aiki da matan da basa sanya hijabi. Bugu da kari, wasu fitattun jarumai da dama sun fuskanci tuhuma kan karya doka ta hanyar kin rufe jikinsu, ciki har da jaruma Azadeh Samadi.
Amurka ta nuna damuwa kan rahotannin sabon matakin murkushe mata a Iran game da sanya hijabi na tilas. Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka Matthew Miller ya ce "da alama gwamnatin ba ta koyi komai ba daga zanga-zangar da aka yi a baya-bayan."
Jami'in kula da harkokin tsaro na kasa kan hanyoyin sadarwa John Kirby ya ayyana cewa, "ya kamata matan Iran su zabi yadda za su yi addininsu da yadda za su yi shiga a bainar jama'a." Ya kara da cewa tuni Amurka ta sanya wa jami'an 'yan sandan da'a na Iran takunkumi da wasu hukumomi da ke da hannu wajen murkushe masu zanga-zanga da suka yi sanadiyar mutuwarsu wasu kuma suka jikkata. "Idan muka ga akwai bukatar daukar karin matakai don kara hura wa gwamnatin wuta to zamu yi," a cewar shi.
Wannan shi ne sharhin Muryar Amurka da ya bayyana muku ra'ayin gwamnatin Amurka.
Dandalin Mu Tattauna