Kotun Koli da ke Abuja, babban birnin Najeriya, ta yanke hukuncin cewa dalibai Musulmi mata da ke zuwa makarantun firamare da sakandare za su iya saka hijabi ba tare da sun fuskanci wata tsangwama ba a jihar Legas.
A ranar Juma’a kotun mai alkalai bakwai ta yanke wannan hukunci inda biyar suka yi na’am yayin da biyu suka nuna adawa.
Kotun kolin ta jaddada hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke, wanda ya nuna cewa an nuna wariya da tsangwama akan dalibai Musulmi idan aka haramta musu saka hijabi a jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya.
Wannan shari’a ta samo asali ne daga takaddamar da aka yi da wata daliba mai suna Asiyat Abdulkarim wacce aka haramtawa saka hijabi a wata makaranta Legas a shekarun baya, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce har wata babbar kotu a jihar ta haramta saka hijabi a makarantun.
Sai dai kungiyar dalibai ta Musulmi ta MSSN ta kalubalanci hukuncin a wata kotun daukaka kara inda aka soke wancan hukuncin babbar kotun a 2015.
A shekarar 2016 gwamnatin Legas ta kalubalanci hukuncin kotun daukaka karar a kotun koli inda aka yanke hukunci a ranar Juma’ar nan.
Wannan hukunci ya kawo karshen tsawon shekaru da aka kwashe ana takaddama akan hijabi da dalibai mata Musulmi suke sakawa a makarantun firamare da sakandare a birnin na Eko.