Zaɓukan fidda Gwani da aka yi a Najeriya sun bar baya da kura, a jihar Taraba wata sabuwar baraka ta kunno kai a jam'iyyar PDP, lamarin da ya sa wasu 'yan asalin jihar su ka yi zanga zangar lumana a gaban sakatariyar jam'iyyar da ke Abuja.
Mr. Andison Emos shi ne shugaban matasa na yankin Takum, kuma shi ne ya jagoranci zanga zangar a Abuja, ya ce sun mika korafinsu ne don mahukuntan jam'iyyar su kirawo manyan jihar Taraba su tunatar da su cewa akwai yarjejeniyar da a ka yi da su akan tsarin karɓa karɓa na mulkin Gwamna.
Hon. Kaigama Yuguda tsohon ɗan majalisa ne mai wakiltar Bali a majalisar dokokin jihar Taraba, ya ce rashin bin tsarin karba karba tauye dimokradiyya ne da maida hannun agogo baya.
Ya kara da cewa yanzu yankin Taraba ta kudu ke mulki, a saboda haka ya kamata mulkin ya koma yammacin Taraba saboda lokacin su ne, amma jam'iyyar PDP ta sake fidda ɗan takara daga kudancin jihar wanda hakan ya saɓa alƙawarin da aka yi da su.
Dr. Mahadi Abba, malami ne a jami’ar Modibbo Adama da ke Yola, ya ce tsarin karba-karba ba ya cikin kundin tsarin mulkin Najeriya amma ana yin shi ne don samun daidaito saboda hakan yakan sa wasu 'yan jam'iyyar canza sheka.
Saurari cikakken rahoton Salisu Lado: