Sokoto, Nigeria —
A Najeriya bayan hatsaniyar da tayi sanadin kisan wata daliba a kwalejin koyar da malanta a jihar Sakkwato da ke arewa maso yammacin kasar, kungiyoyi da muhimman jama'a sunyi ta yin allawadai da wannan lamarin da kuma daukar doka a hannu da daliban suka yi, tare da kiran a zauna lafiya.
Sai dai da safiyar yau Asabar wasu matasa sun soma wata zanga zanga wadda daga baya ta soma rikidewa zuwa tarzoma, abinda ya sa gwamnatin jihar Sakkwato ta saka dokar ta baci ta tsawon sa'a 24.
Saurari jawabin gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal: