Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zanga-Zanga Ta Bazu Zuwa Aljeriya Da Yemen


Magoya bayan gwamnatin Yemen (a dama) su na kokarin far ma masu zanga-zangar neman saukar shugaba Ali Abdullah Sale a Sana'a, babban birnin Yemen, asabar 12 Fabrairu 2011.
Magoya bayan gwamnatin Yemen (a dama) su na kokarin far ma masu zanga-zangar neman saukar shugaba Ali Abdullah Sale a Sana'a, babban birnin Yemen, asabar 12 Fabrairu 2011.

Kwana guda a bayan da zanga-zanga ta kori Hosni Mubarak daga kan mulki, 'yan Aljeriya da Yemen su na neman saukar shugabanninsu

Kwana guda a bayan da zanga zanga ta kori shugaba Hosni Mubarak na Masar daga kan karagar mulki, jama'a sun fito a kasashen Yemen da Aljeriya su na neman korara shugabannin kasashen daga kan mulki.

A Sana'a, babban birnin Yemen, dubban masu zanga-zanga sun yi cincirindo a wani dandali su na neman shugaba Ali Abdullah Saleh da yayi murabus. Daga bisani, sun doshi ofishin jakadancin Masar dake Yemen, amma sai suka yi arangama da wasu mutane dauke da sanduna da suka far musu. Ba a san ko mutanen da suka fito da sandunan 'yan sanda en ko kuma magoya bayan gwamnati ba.

Da alamun ‘yan zanga-zangar na kasar Yemen su na hallara ne a Jami’ar Sana’a da kuma dandalin Tahrir, wanda sunansa daya da dandalin nan na birnin al-Qahira da ya zamo cibiyar masu zanga-zangar kin jinin gwamnatin Masar.

Shi ma shugaban na Yemen, kamar tsohon shugaba Mubarak, ya shafe shekaru fiye da 30 yana mulkin kasar. A wani yunkurin neman kwantar da wutar zanga-zanga a kasarsa, shugaba Ali, wanda tun shekarar 1978 yake mulkin kasar Yemen, yayi alkawarin cewa zai sauka idan wa’adinsa ya kare a shekarar 2013.

Masu zanga-zanga, asabar 12 Fabrairu, a kasar Aljeriya
Masu zanga-zanga, asabar 12 Fabrairu, a kasar Aljeriya

A halin da ake ciki kuma, an girka ‘yan sanda wajen dubu 30 a Algiers, babban birnin Aljeriya, domin hana abkuwar wata zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati da aka shirya yau asabar, wadda haramun ce a karkashin dokar ta bacin da aka shafe shekaru 19 ana aiki da ita a kasar.

Amma rahotanni sun ce duk da kasancewar ‘yan sandan, mutane kimanin dubu 2 sun fito kan tituna su na neman da a kawo karshen aiki da dokar ta baci, da kuma karshen mulkin shugaba Abdelaziz Bouteflika. Gwamnatin Aljeriya ta yi alkawarin kawar da dokar ta bacin nan gaba.

A can kasar Bahrain kuma, ‘yan raji sun yi kiran da a fara zanga-zanga a ranar litinin. Amma a wani yunkurin lallashin masu niyyar yin zanga-zangar, jiya jumma’a sarkin kasar ta Bahrain ya bada sanarwar cewa gwamnati zata bayar da kyautar dala dubu daya, kimanin Naira dubu 150, ga kowane gida a kasar, domin nuna irin godiyar Sarki ga al’ummar Bahrain.

XS
SM
MD
LG