A jamhuriyar Nijar mata su ne suka fi fuskantar matsaloli duk da kokarin da wasu kungiyoyi da masu hannu da shuni su keyi na fitar dasu daga kangin talauci.
A firar da wasu mata suka yi da Muryar Amurka sun ce suna sana'o'i domin taimaka wa kansu da 'ya'yansu.
Wata tace suna sana'ar sayar da lemo da ruwan sanyi kuma kamar yadda tace tubarkalla. Tana sayar da lemun a gida yaranta kuma na kai mata kasuwa su sayar.
Da sana'arsu matan suna taimakawa rayuwarsu da 'ya'yansu da mazajensu. Matan sun ce zamani ya canza. Ba lallai ba ne komi su sakar ma mazajensu suna jiran su yi masu ba. A cikin sana'o'in nasu suna taimakawa 'ya'yansu zuwa makarantun Islama da na boko. Suna taimakawa da harkokin litattafensu.
Wata tace yau shekara biyu ke nan da mijinta ya rasu ya barta da 'ya'ya amma saboda dogaro ga sana'arta bata taba zuwa neman taimako ba wurin wani. Da sanarta take ciyar da 'ya'yanta da kuma biyan wasu bukatu.
Duk da matan dake sana'o'i suna taimakawa kansu akwai wasu da basu san wata ranar mata ba. Wata tace ita bata taba cin moriyar ranar mata ba.
Ga karin bayani.