Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Yanke Wa “Mama Boko Haram" Da Wasu Mutane 2 Hukumcin Daurin Shekaru 10


Mama Boko Haram
Mama Boko Haram

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, shiyyar Maiduguri, ta samu nasara a karar da ta shigar kotu inda aka yanke wa Aisha Alkali Wakil, wacce  aka fi sani da "Mama Boko Haram" da Saidu Daura, da kuma Prince Lawal Shoyode. hukuncin daurin shekaru goma.

Mai shari’a, Umaru Fadawu na babbar kotun jihar Borno ne ya yanke musu hukuncin daurin shekaru goma Litinin, 12 ga watan Fabrairu, 2024.

Lauyan mai gabatar da kara, A.I Arogha ya gabatar da shaidu hudu tare da gabatar da wasu takardu goma sha bakwai a matsayin shaida a gaban kotu yayin sauraron karar da duka basu wanke wadanda ake tuhumar ba.

Sakamakon haka, Mai shari’a Fadawu ya yanke musu hukuncin daurin shekaru goma a gidan yari bisa laifin hada baki, sannan ya umarce su da su biya N40m a matsayin diyyar wadanda abin ya shafa.

Idan ba a manta ba, an fara gurfanar da wadanda ake tuhumar ne a ranar 14 ga Satumba, 2020 a gaban Mai shari’a Kumaliya, kan tuhume-tuhume biyu da suka shafi hada baki da yaudara wajen karbar kudi har N40, 000,000.00 (Naira Miliyan Arba'in) daga wani kamfani da cewa za su samar masu da wadansu kayan aiki amma suka danne kudin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG