Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hannun Jarin Access Holdings A Najeriya Ya faɗi Da Kaso 6.26 Cikin Dari Yayin Da Ake Ci Gaba Da Makokin Herbert Wigwe


Herbert Wigwe
Herbert Wigwe

Farashin hannun jari Access Holdings na Najeriya ya fadi da kaso 6.26 a yau yayin da masu hannun jari a kamfanin ke alhinin rasuwar Herbert Wigwe.

WASHINGTON, D. C. - A makon da ya gabata ne Access Holdings ya samu raguwar kaso 2.25 cikin dari na farashin hannun jarin, ya kuma yi asarar karin N1.55 bayan rufewar hukumar hada-hadar hannayen jari a kan N23.20, daga N24.75 a ranar Juma’ar da ta gabata.

Hannun jarin na Access ya samu karuwar saya da sayarwa, a yayin da shine mafi girman hannun jari a cikin kasuwar hada-hadar, in da take da tare da kashi miliyan 24.90 na ACCESSCORP. Dangane da kimar, ACCESSCORP ta samu darajar cinikin Naira miliyan 575.1.

Saboda rasuwar Herbert Wigwe na ba zato ba tsammani, Access Holdings a hukumance ta bayyana aniyar ta na nada shugaban riko.

Yayin da kungiyar ke tafiyar da wannan lamarin na ba zato ba tsammani, ana kokarin tsara tsari na gudanar da aikin gaggawa cikin gaggawa kuma ana shirin aiwatarwa.

A matsayinsa na shugaban kamfanin Access Holdings, Wigwe ya bunkasa kadarorin bankin zuwa Naira tiriliyan 21.4 a cikin Q3 2023, wanda hakan ya sa ya zama banki mafi girma a Najeriya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG