Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Jawo Al'umma Cikin Tsarin Tsaro Domin Inganta Harkokin Tsaron


Jami'an Tsaro.
Jami'an Tsaro.

Wani lauya mai zaman kansa a jihar Kaduna yace idan ana son a shawo kan tabarbarewar harkokin tsaro to wajibi ne a jawo al'umma cikin tsarin tsaron kasa.

Malam Buhari Bello lauya mai zaman kansa yace idan har ana bukatar magance matsalar tsaro a Najeriya wajibi ne a jawo al'umma cikin tsarin tsaron da yace yanzu ya riga ya tsumbula cikin wani hali.

Malam Bello ya gabatar da wata kasida a wani taro akan matsalar tsarin tsaro da 'yancin Biladama a Najeriya. Yace ba 'yan kungiyar Boko Haram kadai ba ne suka karya dokokin cikin gida da na kasa da kasa. Su kansu jami'an tsaron Najeriya nada nasu laifukan.

Duk abubuwan da 'yan Boko Haram suke yi sun saba ma dokoki cikin gida da na waje. Haka ma wasu abubuwan da jami'an tsaron kasar suke yi. Yace idan ana son a shawo matsalar dole sai an hada da mutane. Kana duk wanda ya karya doka ya fuskanci shari'a ba sani ba sabo.

Shi kuma Dr Sadiq Abubakar Umar Gombe cewa yayi idan aka cigaba da yin sakaci da harkokin tsaro a arewa babu shakka yaki zai zo ya ci kowa, kudu da arewa yamma da gabas. Babu yankin kasar da yaki zai bari. Ba arewa kadai 'yan Boko Haram ke tayar da kayar baya ba. Cikin satin nan wasu 'yan tsiraru suka farma gidan telibijan na Enugu da suna neman kafa kasar Biafra.

Abubuwan da suke faruwa abubuwa ne da suke nuna cewa gazawa ne na shugabanci amma mutane sun gagara su bude idanunsu su kalla ko su yi magana. Suna ganin abun ne daga wani karamin bangare maimakon su duba kasar gaba daya. Da sun sani cewa kasa ce da Allah ya dora masu nauyinta da ba'a shiga irin wannan halin ba.

Dr Usman Bugaje shugaban bunkasa bincike ta arewa ita ce ta shirya taron yini biyu a Kaduna. Yace taro ne da ake son manyan arewa da masu ruwa da tsaki a yankin su duba abubuwan dake faruwa su hada kai su tsara matakan da yakamata a bi kafin abun da ake gudu ya farma arewa da kasa gaba dayanta. Tarihi ya nuna cewa idan gwamnati ta gaza to al'umma su taru su yi hobbasan abun da za'a yi idan ba haka ba to saidai Allah ya kiyaye abun da ka biyo baya. Hakan ya faru a kasar Somaliya. Bayan shekara 25 da suka yi suna fada har yanzu babu zaman lafiya.

Ga rahoton Isah Lawal Ikara.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:31 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG