Kawo yanzu dai ba'a san yadda ta kaya ba tsakaninsu. Wasu mazauna garin sun ce 'yan Boko Haram suka fara kai farmaki akan sansanin sojoji dake garin. Bayan sun kawo harin jirgin saman sojoji ya kawo doki ya zubawa 'yan kungiyar wuta. Suma sojoji sun tara kansu sun bi mayakan dajinsu da suke buya ciki.
Mazauna yankin na kauracewa gidajensu musamman ganin yadda 'yan bindigan ke awon gaba da matasa maza. Su kan tilasta masu su zama 'yan kungiyarsu.
Yanzu dai rundunar soja ta ashirin da uku dake Yola ta fitar da sanarwar hana gidajen kallon kwallon kafa budewa domin kauracewa duk wani abun da ka iya faruwa gaf da fara gasar cin kofin duniya. Rundunar ta ce ta dauki matakin ne sakamakon rahotanin siri dake cewa akwai wani shirin kai hari a gidajen kallon kwallon inda jama'a ke taruwa.
Gwamnatin jihar ta Adamawa ta bukaci al'ummar jihar su bada hadin kai da rundunar sojan. Ta kuma roki gwamnatin tarayya ta tallafawa wadanda zasu rasa sana'arsu sakamakon dokar ta sojoji.
Malam Ahmed Sajoh kakakin gwamnatin jihar Adamawa yace a cikin yanayin dokar ta baci shugaban rundunar soja shi ne shugaban tsaro a jihar. Duk shawarar da ya bayar dole ne a bi domin a samu zaman lafiya. Yace a taimakawa mutane da tallafi ba nuna karfi ba kawai.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.