Donald Trump ya sake karbar rantsuwar kama aiki a sabon wa’adin mulki na shekaru 4 a fadar White House.
Donald Trump ya zama shugaban kasar na 47 biyo bayan nasarar da ya samu a zaben da ya gudana a watan Nuwamban daya gabata.
Zababben mataimakin shugaban kasa JD Vance ya karbi rantsuwar kama aiki kafin aka rantsar da Shugaban Trump.
Trump ya ce zai fitar da jerin umarnin zartarwa da za su fasalta yadda Amurka za ta shawo kan batun 'yan kasa da baki, kamar yadda ya bayyana a yau Litinin jim kadan bayan rantsar da shi.
Shugaban Amurka na 47 din zai fara aiki nan take da jerin umarnin zartarwa da aka tsara domin matukar rage yawan bakin hauren dake shiga kasar.
"Da fari, zan ayyana dokar ta bacin kasa akan iyakarmu ta kudu, a cewar Trump.
"Zamu dakatar da shigowa kasarmu ta barauniyar hanya nan take, sannan zamu fara aikin mayar da milyoyin baki masu aikata miyagun laifuffuka zuwa kasashensu da suka fito.
"Zan aika dakaru zuwa iyakarmu ta kudu domin dakile mummunan yunkurin mamaye kasarmu," a cewarsa.
Trump ya kasance wanda ya aikata babban laifi na farko daya zama shugaban Amurka, bayan da wata kotu a bara ta same shi da laifi a tuhume-tuhume 34 dake da nasaba da shirya bayanan kasuwancin bogi domin boye toshiyar bakin dala 130, 000 daya biya wata jarumar fina-finan batsa stormy daniels, duk da cewar alkalin yaki amincewa ya hukunta shi ta kawone hali.
Dandalin Mu Tattauna