A yayin da Donald Trump ya soma wa’adin mulkinsa a karo na biyo, kasashen Turai na ci gaba da nazarin yadda wasu manufofinsa za su shafi dangantakarsu da Amurka, musamman a fannin cinikayya.
Ga Jamus, kasa mafi karfin tattalin arziki a Turai, manufofin Trump kan haraji da kayan fitarwa na haifar da fargaba.
Muhammad Laminou Sumaila Abba, masanin kimiyyar cinikayya ta zamani da na’ura mai kwakwalwa a Jamus, ya yi tsokaci kan abin da zai biyo baya baya a dangantakar kasar da Jamus.
Hakazalika, wani babban batun da ke jan hankalin kasashen na Turai shi ne, yakin da ake gwabzawa a tsakanin Rasha da Ukraine.
Shugaba Trump ya yi ikirarin cewa zai kawo karshen wannan yakin cikin gaggawa idan aka ba shi dama.
Sai dai, Malam Muhammad Laminou na ganin abin kamar da wuya
"Idan aka yi la’akari da girman rikicin da kuma bambancin ra’ayin bangarorin da ke rikicin" a cewarsa.
Martanin Kasashen Turai Kan NATO
A Jamus, barazanar da Trump ya yi na rage kudin da Amurka ke bayar wa ga Kungiyar Tsaro ta NATO ta haifar da fargaba.
Dalibi Huzaifa Yahuza, wanda ke bibiyar siyasar duniya ya ce, tsaron duniya na cikin hadari muddin shugaban ya janye taimakon Amurka.
Ra’ayoyin Jama’a a Turai
Muryar Amurka ta ji ra’ayoyin wasu mazauna Turai kan sabuwar gwamnatin Trump.
Nargis Shah, wata ‘yar Iran da ke zaune a Turai ta bayyana damuwarta kan makomar Iran
An dai zura idanu don ganin yadda wa’adin Shugaba Donald Trump zai kaya.
Shi da jam’iyyarsa ta Republican na da rinjaye a majalisar dokokin Amurka, kuma suna da manufofi masu cike da buri amma duk da haka, jam’iyyar Democrat ta bayyana aniyarta ta kalubalantar wasu daga cikin wadannan manufofin.
~ Ramatu Garba Baba ~
Dandalin Mu Tattauna