Joe Biden ya kamala wa’adin mulkin shi a matsayin shugaban kasa a jihar South Carolina, a jiya lahadi, inda bukaci Amurkawa su yi "fatan samun ci gaba mai dorewa nan gaba."
Wuni daya gabanin rantsar da zababben shugaban Amurka, dan jam'iyyar Republican Donald Trump, Biden ya yi jawabin bankwana a jihar South Carolina, jiha mai muhimmanci a siyasar Amurka, musamman bayan nasarar da ya samu a zaben fidda gwani na jam'iyyar Democrat a shekarar 2020, wanda ya sanya shi cimma burin shi na zama shugaban kasar Amurka.
Biden ya yi magana a ikilisiyar cocin Baptist, a game da dalilin da ya sa ya shiga hidimar jama'a, ya bayyana cewa, Martin Luther King Jr. da Robert F. Kennedy Jr. sune mutanen da yake koyi da su a siyasa, sannan ya yiwa al'ummar jihar South Carolina godiya saboda irin goyon bayan da suke bashi.
Dandalin Mu Tattauna