Masana kimiyyar siyasa da ‘yan diflomasiyya a Afirka na sharhi kan dawowar shugaba Donald Trump kan karagar mulki.
Wannan ya zama mai muhimmanci don doguwar huldar diflomasiyya da ke tsakanin Afirka da Amurka.
A Najeriya, masanin kimiyyar siyasa na jami’ar Bayero Dakta Sa’idu Ahmed Dukawa ya ce ya na ganin akwai raguwar barazanar targaden huldar Najeriya da Amurka a bangaren diflomasiyya, shige da fice, tsaro da sauransu.
A saurari rahoton Nasiru Adamu el-Hikaya kan dawowar Trump shugabancin Amurka.
A Kamaru, Washington da Yaoundé suna da tsohuwar alaka tun kafin Kamaru ta samu ´yancin kanta daga mulkin mallaka a 1960.
Kasar Amurka ita ce kasar da ta fi kowacce bayar da agajin jin kai ga kasar Kamaru tare da samar da sama da dala miliyan 650 tun daga shekarar 2014, ciki har da rarraba kayan masarufi da ayyukan inganta lafiyar mata da kananan yara ga sama da mutane miliyan 1.4 da suka amfana.
Al'ummar Ghana kamar sauran kasashen duniya, inda suka bayyana muhimmanci da matsayin kasar Amurka a duniya.
A jamhuriyar Nijar, masana na gargadin gwamnatin Trump ta lura da yadda kasashe abokan hamayyar Amurka wato Rasha, China da Iran da sauransu ke kokarin samun matsuguni a Nijar watakila a bisa hasashen kakace ma’adinan kasa.
Dandalin Mu Tattauna