Cibiyar Nazarin Dabaru ta Afirka ta ce yadda ake yada labaran karya da gangan ko cikin kuskure a Afirka, ya ninka kusan sau hudu tun daga shekarar 2022, lamarin da ke kawo tarnaki ga zaman lafiya da dimokradiyyar wasu kasashe da muka duba: Kamaru, Congo, Mozambique, Malawi da Ghana.