Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Obama Ya Shiga Tsaka Mai Wuya Kan Takarar Biden


Shugaban kasar Amurka Joe Biden da tsohon shugaban kasar Barack Obama
Shugaban kasar Amurka Joe Biden da tsohon shugaban kasar Barack Obama

Tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya shiga tsaka mai wuya kan yadda zai shiga tsakani dangane da kiraye-kirayen da ake yi wa Shugaba Joe Biden na ya janye takararsa.

A cikin 'yan kwanakin nan, Obama ya karbi korafe-korafe daga shugabannin majalisa, gwamnonin jam’iyyar Democrat da kuma manyan masu ba da taimako da mika ra'ayinsu game da makomar yakin neman zaben Biden sakamakon mummunar muhawarar da ya yi a ranar 27 ga Yuni da Donald Trump.

Joe Biden
Joe Biden

Duk da ya saurari wadannan kuken, Obama ya dage cewa Biden ne yake da hurumin ya yanke shawarar ci gaba da kasancewa a takarar, a cewar mutane da yawa da suke da masaniya kan lamarin, wadanda suka nemi a sakaya sunayensu.

Wannan wani lokaci ne da Obama ke bukatar ya samar da daidaito a matsayinsa na dattijo a jam’iyyar kan yadda zai magance korafin wadanda suka kai masa korafi ba tare da ya ci dunduniyar tsohon mataimakinsa ba.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG