Duk da yake muhawara tsakanin ‘yan takarar shugaban kasa ta zama al’ada a zaben Amurka, muhawarar ta jiya ta zama ta tarihi a fannoni da dama, kasancewa, wannan ne karon farko da aka yi muhawara tsakanin wani tsohon shugaban kasa da shugaban kasa mai ci, banda haka kuma, ‘yan takarar, sun yi muhawararsu ta farko ne jiya, kafin jam’iyunsu su tsaida su takara a hukumance, haka kuma, ko da wanene zai lashe zabe bana, zai kasance shugaban kasa mafi yawan shekaru a tarihin amurka.
David Bodington, wani tsohon soja dan shekaru 85, ya bayyana cewa, ya riga ya yanke hukumci kan dan takarar da zai zaba, sai dai muhawarar ta dauki hankali shi domin jin ko akwai wani abu na dabam da ‘yan takarar za su fada.
"A wuri na, karin tabbaci ne cewa, zan zabi Biden, zan zabe shi ne domin babu yadda lamiri na zai amince da zaben Trump sabili da na san tarihinshi. Ba Biden ba ne zabi nan a farko, zan so ganin Bernie Sandars. Zan gwammace in zabi Bernie Sandars kafin in zabi Biden. Sai dai da yake Biden ne zai zama dan takarar, zaben zai kasance tsakanin Biden da Trump ne da kuma Kennedy Jnr, amma shi Kennedy yana bata lokacin shi ne kawai. Zaben zai kasance tsakanin Biden ne da Trump kuma ban ga yadda zan zabi Trump ba."
A nashi bayanin. Dr Sylvanus Okere, wani Ba’armuke dan asalin Najeriya ya bayyana cewa, duk da yake yanzu baya goyon bayan wata jam’iya, zai zabi Trump ne bana bisa dalilin cewa, tsohon Shugaban kasar ya fi bada fifiko kan batun kare kan iyakoki da kuma matsalar tsaaro. Ya ce,
"A matsayina na kwararre a fannin tsaro, bana wasa da abinda ya shafi tsaro. Kan iyakokinmu suna bude babu tsaro, miyagu suna shigowa, abubuwa da basu da kyau da yawa suna shigowa. Zai zama da mamaki a ji ina fadin haka kasancewa ni dan cirani ne Ba’amurke dan asalin Najariya. Mutane za su ce, menene ya sa baka so wadansu su shigo kasar? Ya kamata mutane su shigo kasar ta hanyar da doka ta tsara. Duk kasar da bata kare kan iyakarta ba, ba kasa bace."
Dr Okere ya kuma bayyana cewa a matsayinshi na wanda ya mallaki karamin kamfani, tattalin arziki yana da muhimmanci ga Shugaban kasar da zai zaba. Ya ce, "Farashin komi ya tashi a kasar nan, kayan masarufi, madarar jarirai, man fetir komi ya yi tsada, dukanmu muna shan wahala, amma mutane sabili da siyasa ba zasu fadi gaskiya ba. Gaskiya mutane basu iya cin abinci yadda su ke so, kuma a matsayina na mai karamin kamfani, kanaanan kamfanoni da masana’antu suna shan wuya. Saibili da haka ya kamata mutane su daina siyasa da batun su nunawa mai laifi laifinshi. Sauran kasashe suna yi mana dariya. Saboda haka muna son shugaban kasa da zai nuna shi shugaban kasa ne, sabili da haka zan zabi manufa ne ba mutum ba. Duk wanda yake da manufa da tsare-tsare da suka fi dacewa, shi ne zan zaba. Zan yi zabe ne a kan tattalin arziki da kuma tsaro."
Shi kuwa Mallam Jiban Saulawa mazaunin jihar West Virginia ya bayyana cewa, dan takarar da zai iya kawo karshen yakin yankin Falasdinawa shi ne zai ba kuri’a.
Za a gudanar da babban taron Jam’iyar Democrat na kasa, lokacinda jam’iyar za ta tsayar da dan takararta a hukumance daga ranar 19 zuwa 22 ga watan Agusta a Chicago, Illinois. Bisa ga al'ada, saboda a halin yanzu Jam'iyyar Democrat ce ke mulki, za a gudanar da babban taronta bayan na Jam'iyyar Republican na wanda aka za a gudanar daga 15 zuwa 18 ga Yuli a Milwaukee, Wisconsin.
Saurari cikakken
rahoton:
Dandalin Mu Tattauna