Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa
Afirka

Gwamnatin Nijar Ta Hana Kungiyoyin Kare Hakkin 'Dan Adam Kai Ziyara Gidajen Yarin Kasar


Sojojin juyin mulki a Jamhuriyar Nijar
Sojojin juyin mulki a Jamhuriyar Nijar

Gwamnatin rikon kwaryar Nijar ta hana kungiyoyin kare hakkin 'dan adam na cikin gida da na kasa da kasa kai ziyara a gidajen yarin kasar har sai yadda hali ya yi.

Haka kuma a tsawon wannan lokaci matakin ya saka wa irin wadannan kungiyoyin haramcin bada tallafi da ayyukan fadakarwar da aka saba gudanarwa domin fursinoni.

Hukumomin ba su bayyana dalilin yanke wannan shawara ba, lamarin da ya janyo aza ayar tambaya daga ‘yan rajin kare hakkin bil adama.

Ta hanyar wata takardar da ya aike wa manyan masu shigar da kara a kotun daukaka kara ta Yamai da ta Zinder da ta Tahoua Procureurs Generaux da masu shigar da kara a kotun Tribunal manya da kanana Procureurs de la Republique da shugabanin gidajen kaso Regisseurs, Ministan Shari’a da kare hakkin 'dan adam mai shari’a Alio Daouda ya sanar da wadannan jami’ai cewa daga yanzu gwamnati ta hana kungiyoyin kare hakkin 'dan adam na cikin gida da na kasa da kasa kai ziyara a gidajen kaso sai baba ta gani.

Kaka Touda Goni wani mamba a kungiyar fafutika ta Alternative Espace Citoyen ya fassara matakin a matsayin koma bayan sha’anin kare hakkin 'dan adam a kasar.

Ministan ya kuma dauki matakin hana irin wadannan kungiyoyi gudanar da ayyukan bada tallafi da taron fadakarwa da aka saba shiryawa a gidajen yari, koda yake kuma bai fadi dalilan gwamnati na bullo da wannan da wancan mataki ba.

A ra’ayin shugaban kungiyar kare hakkin jama’a Kulawa da Rayuwa, Hamidou Sidi Fody abin na iya shafar yanayin walwalar mutanen da ke kulle a kurkuku.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma :

Gwamnatin Nijar Ta Hana Kungiyoyin Kare Hakkin 'Dan Adam Kai Ziyara Gidajen Yarin Kasar.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG