Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Biden Zai Sanar Da Sabon Shirin Kare Mutanen Da Su Ka Auri Amurkawa


Israel Palestinians
Israel Palestinians

A yau Talata ake sa ran Shugaban Amurka Joe Biden zai sanar da wani gagarumin sabon shirin da zai kawar da barazanar mayar da dubban mutanen da suka auri yan kasar Amurka zuwa gida.

Wannan wani mataki ne da ya shafi batun shigowa kasar a shekarar zabe, da tuni da dama da ga cikin yan Democrat su ka nema.

Biden ya marabci wani buki a fadar white house, na wani shirin da aka assasa a zamanin Obama da ya bayar da kariya ga iza keyar matasan da suka shugo kasar da ba’a dauki bayanan su ba zuwa kasashen su, zai kuma sanar da sabon shirin a lokacin, kamar yadda wadansu mutane uku da fadar white house ta yiwa bayani ga me da shirin su ka bayyana.

Masu zanga-zangar neman samun damar zama 'yan kasar Amurka
Masu zanga-zangar neman samun damar zama 'yan kasar Amurka

Biyu da ga cikin mutanen da aka yi wa bayanin, sun bayyana cewa, tsarin zai bada dama ga kusan ma’aurata 490,000 su mika takardun neman mafaka a karkashin shirin, wanda zai kange su daga iza keyar su zuwa kasashen su, da ba su iznin yin aiki, idan har sun kai shekaru a kalla 10 a cikin kasar.

Duk mutanen dai sun yi magana ne bayan da suka nemi a saya sunayen su, saboda ba a basu damar tattauna batun a bainar jama’a ba.

Wadansu mutane ranar da su ka zama 'yar kasar Amurka
Wadansu mutane ranar da su ka zama 'yar kasar Amurka

Fadar white house ta ki cewa uffan akan sanarwar, lokacin da aka nemi ta yi hakan a jiya Litinin.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG