Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Zai Mikawa Majalisa Sabon Kudirin Mafi Karancin Albashi Nan Ba ​​Da Jimawa Ba  


Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, a ranar Ma'aikata ta Duniya
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, a ranar Ma'aikata ta Duniya

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a jawabinsa na ranar Dimokradiyya a yau Laraba 12 ga watan Yunin 2024 wanda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauya zuwa duk ranar 12 ga watan Yunin shekara-shekara sabanin ranar 29 ga watan Mayun da aka saba a baya.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa kungiyar kwadagon kasar cewa nan ba da jimawa ba za a aika da kudirin doka kan sabon mafi karancin albashin ma’aikata na kasa zuwa majalisar dokokin kasar domin amincewa da shi.

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a jawabinsa na ranar Dimokuradiyya a yau Laraba 12 ga watan Yunin 2024 wanda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauya zuwa duk ranar 12 ga watan Yunin shekara-shekara sabanin ranar 29 ga watan Mayun da aka saba a baya.

A cewar shugaba Tinubu a yayin jawabinsas, gwamnati ta yi shawarwari cikin aminci tare da Kungiyoyin Kwadago kan sabon mafi karancin albashi na kasa kuma nan ba da jimawa ba “za mu aika da wani kudurin doka na zartarwa ga Majalisar Dokoki ta kasa don sanya abin da aka amince da shi a matsayin wani bangare na dokar mu na tsawon shekaru biyar ko kasa da haka don sabuntawa,” in ji Shugaban.

Haka kuma, shugaban ya taya dukkan ‘yan Najeriya murnar ganin wata sabuwar ranar dimokuradiyya a yau, 12 ga watan Yunin shekarar 2024, wanda a wannan shekarar aka cika shekaru 25 na komawa tsarin mulkin dimokaradiyyar a Najeriyar.

A cewar shugaban, a wannan rana irin ta yau shekaru 31 da suka gabata ne Najeriya ta shiga cikin ayyukan zama al'ummar mai tafiya a tsarin mulkin dimokradiyya ta gaskiya kuma mai dorewa, yana mai cewa, shiga cikin wannan tsarin mulki na da wahala da haɗari.

Lamarin da a waccan lokaci, an kwashe shekaru shida masu tsanani da suka biyo baya, inda aka yi gwagwarmayar kwato wa ‘yan Najeriya hakokkin su na ’yan Adam da ikon Allah.

Tinubu yace, a yayin gwagwarmayar tabbatar da tsarin mulkin dimokradiyya ya dore, an rasa manyan jarumai a hanya, kuma a yayin fafutuka, wanda ya lashe zaben shugaban kasa a ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1993, Cif MKO Abiola, wanda shi ne mafi girman alamar gwagwarmayar dimokradiyyar mu, da matarsa, Kudirat Abiola da marigayi Janar Shehu Musa Yar’Adua da Pa Alfred Rewane, da dai sauransu sun sadaukar da rayuwarsu don ganin dorewar dimokradiyya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG