Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

RANAR DIMOKRADIYYA: Tinubu Zai Yi Wa ‘Yan Najeriya Jawabi


Shugaban Najeriya, Bola Tinubu (Hoto: Facebook/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu (Hoto: Facebook/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

Shugaba Bola Tinubu zai yi jawabi ga al’ummar kasar kai tsaye a ranar Laraba domin murnar cika shekaru 25 da dawowa mulkin dimokradiyya a Najeriya.

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

Don haka ne ya umarci gidajen talabijin, rediyo, da sauran hanyoyin sadarwa na zamani da su hada kai don yada jawabin wanda gidan talabijin ta kasa (NTA) da gidan Rediyon Tarayya (FRCN) zasu watsa.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG