Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamna Uba Sani Ya Yi Wa Fursunoni 110 Afuwa A Jihar Kaduna


Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani
Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya bayar da umarnin a saki fursunoni 110 daga gidan gyaran hali da ke jihar, a zaman wani bangare na bikin ranar dimokradiyya na bana da kuma murnar cika shekara guda a kan karagar mulki.

WASHINGTON, D. C. - Gwamnan wanda shi da kansa ya ziyarci gidan gyaran hali na jihar Kaduna tare da lauyan kare hakkokin bil’adama, Femi Falana (SAN), ya bayyana bukatar a yi garambawul a gidajen gyaran hali da ke jihar Kaduna.

Ya kara da cewa matakin da ya dauka na sakin fursunonin 110 ya je daidai da ikon da ya ke da shi a karkashin tanadin sashe na 212 na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999.

A nasa bangaren, Falana ya yaba wa Gwamna Sani bisa yadda ya yi wa fursunonin afuwa.

Ya kuma yi kira ga manyan alkalan jihohi da su ba da umarnin a rinka gudanar da bincike lokaci zuwa lokaci a ofisoshin ‘yan sanda a jihohinsu don duba batun tsare mutane ba bisa ka’ida ba, ya kuma yi kira ga gwamnonin jihohin kasar da su ba da fifiko wajen gyaran cibiyoyin gyaran hali da ke jihohinsu.

An dai gina gidan gyaran hali na Kaduna ne a shekarar 1915, wanda zai iya daukar fursunoni 500.

Amma a halin yanzu, cibiyar tana da fursunoni sama da 3,000 a cikin ta, yayin da wadanda ke jiran a yanke musu hukunci suka kara yawan adadin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG