ABUJA, NIGERIA - Wannan ya biyo bayan rashin cimma matsaya da banaren gwamnati kan karin mafi karancin albashi da janye karin farashin wutar lantarki.
Zaman da gamayyar kungiyoyin kwadagon ta yi da shugaban majalisar dattawa Godswull Akpabio da sa bakin majalisar wakilai bai cimma nasarar dakatar da tafiya yajin aikin ba.
Akpabio ya ce za su ci gaba da rokon 'yan kwadagon don su sauya matsaya.
Shugaban kungiyar kwadago ta TUC, Komred Festus Osifo, ya ce sun yanke matsayar aukawa yajin aikin har zuwa lokacin da gwamnati ta saurari bukatunsu.
Shima mukaddashin sakataren TUC, Hassan Salihu Anka, ya ce ba ja da baya ga yajin aikin.
Nan take shugaban wata kungiya ta raya arewa maso gabashin Najeriya, Abdurrahman Kwacam, ya caccaki matsayar 'yan kwadagon da ya ke ganin don muradun kashin kai ne "da zarar gwamnati ta biya mu su bukata za su janye yajin aikin kuma sun kara batun wutar lantarki ne don neman goyon bayan jama'ar kasa. Ina ganin gwamnati za ta kife idan ta amince da biyan makudan kudi na mafi karancin albashin da su ke bukata."
Dr. Yunusa Tanko na jam'iyyar kwadago Leba ya ce rashin tsarin gwamnati ya sa rayuwa na neman gagarar talakawa don haka biyan karancin albashin zai rage matsalar ce kawai.
Yayin da gwamnati ke amincewa da biyan Naira N60,000 wato kasa da rabin dalar Amurka; 'yan kwadago na bukatar N477,000 wanda saukowa kasa ne daga N615, 000.
Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-hikaya:
Dandalin Mu Tattauna