Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Kwadago Sun Janye Yajin Aiki A Fadin Najeriya


Hadaddiyar Kungiyar Kwadago A Najeriya Ta Dakatar Da Yajin Aiki
Hadaddiyar Kungiyar Kwadago A Najeriya Ta Dakatar Da Yajin Aiki

Shugabancin kungiyar kwadago ta dakatar da yajin aikin da ake yi a duk fadin kasar, bayan tattaunawar da suka yi da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, malam nuhu ribado.

ABUJA, NIGERIA - Shugabannin kungiyoyin kwadagon sun yanke shawarar dakatar da yajin aikin da suka fara a duk fadin kasar a ranar 14 ga watan Nuwamba, 2023.

Yajin aikin ya fara ne a matsayin zanga-zangar nuna adawa da harin da aka kaiwa shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya Joe Ajaero, an yanke shawarar kawo karshen yajin aikin ne bayan wani taro tare da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu.

Lamarin da ya kai ga yajin aikin ya faru ne a ranar 1 ga watan Nuwamba yayin da Ajaero da wasu shugabannin kwadago suka yi gangami a garin Owerri na jihar Imo, inda suka nuna rashin amincewarsu bisa zargin take hakkin ma’aikata da gwamnatin jihar ke yi.

Taron dai ya rikide zuwa rudani sakamakon kama Ajaero da ‘yan sanda suka yi da kuma farmakin ‘yan bangar siyasa wadanda ake zargin suna da alaka da Gwamna Hope Uzodinma.

Kungiyar kwadagon ta bukaci da a kore wani Kwamandan da take zargin shi da jagorancin alhakin kai harin. Bayan haka ne kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC da TUC suka kaddamar da yajin aikin a fadin kasar, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin kasuwanci.

Bayan da Nuhu Ribadu ya bayyana kama wasu mutane biyu da ake zargin suna da alaka da harin Ajaero, shugabannin kwadago, a wani taro na musamman, sun yanke shawarar yin la’akari da tabbacin da NSA ya bayar.

Babban sakataren kungiyar AUPCTRE, Kwamared Sikiru Waheed, ya tabbatar da dakatar da yajin aikin na kasa, inda ya umarci mambobin kungiyar su koma bakin aiki a ranar Alhamis 16 ga watan Nuwamba, 2023.

Sakamakon zama da kungiyar ta yi da mai baiwa shugaban kasa shawara Nuhu Ribadu wanda aka sami fahimta da yadda da janye yajin aikin, shugaban kungiyar ta TUC, Festus Osifo da sauran shugabannin kwadago sun bayyana cewa za a tattauna da jami’an gwamnati ga kungiyoyinsu domin ci gaba da daukar matakin gaba.

-Yusuf Aminu Yusuf

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG