Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu ‘Yan Bindiga Sun Sake Awon Gaba Da Akalla Mutane 61 A Kaduna


‘Yan Bindiga
‘Yan Bindiga

Wasu ‘yan bindiga a Najeriya sun yi garkuwa da mutane 61 daga wani kauye da ke arewacin jihar Kaduna, kwanaki bayan da wasu ‘yan bindiga suka sace dalibai 300, kamar yadda mazauna garin suka bayyana a ranar Talata.

WASHINGTON, D. .C - Kungiyoyin da ke dauke da makamai, wadanda aka fi sani da ‘yan bindiga, sun dai shafe shekaru suna tafka barna a arewacin Najeriya, inda suke kai wa mutanen kauye, masu ababen hawa a manyan tituna, da daliban makarantu domin karbar kudin fansa.

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a unguwar Buda da tsakar daren ranar Litinin, inda suka rika harbe-harbe akai-akai, dabarar da suke amfani da ita wajen tsoratarwa, kamar yadda mazauna garin suka bayyana. Sau da yawa ana yin garkuwa da mutanen ne a kananan garuruwan da ke nesa, wanda hakan ya sa mazauna garin suka kasance marsa taimako.

Wani mazaunin garin Lawal Abdullahi ya ce ba ya nan a lokacin da ‘yan bindigar suka kai harin amma matarsa na cikin wadanda aka dauke.

"Matata na cikin mutane 61 da 'yan bindigar suka sace, har yanzu muna sa ran za su nemi kudin fansa kamar yadda suka saba," Abdullahi ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters ta wayar tarho.

Garin Buda dai na da tazarar kilomita 160 daga garin Kuriga, inda a makon da ya gabata aka sace 'yan makaranta.

Kwamishinan tsaron cikin gida na Kaduna da kakakin ‘yan sanda ba su amsa bukatar jin ta bakinsu ba a wannan lokaci.

“Mun dade muna fuskantar wadannan hare-hare, lamarin ya kara ta’azzara, kuma lamarin da yanzu ya tilastawa mazauna kauyuka da manoma da dama tserewa zuwa wuraren da ba su da hadari,” in ji wani mazaunin garin, Danjuma Sale.

Mai-fashin baki kan al’amuran tsaro manjo Yahaya Shinko mai-ritaya ya ce hauhawar hare-haren 'yan-bindigan na da sanadi.

A cewar Manjo Shinko duk lokacin da rayuwa ta yi tsada matsalar tsaro kan karu saboda haka ya ce akwai bukatar gwamnati ta jingine komai ta fuskanci maganar matsalar tsaro.

Ya zuwa safiyar yau Laraba dai har 'yan-bindigan sun bayyana bukatar kudin fansa kafin sakin mutanen da su ka kama ciki har da mai danyen jegon da su ka raba ta da jaririn inji wani mazaunin garin.

-Reuters

A saurari karin bayani daga Isah Lawal Ikara:

Wasu ‘Yan Bindiga Sun Sake Awon Gaba Da Akalla Mutane 61 A Kaduna.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG