KADUNA, NIGERIA - Da safiyar yau Alhamis ne dai 'yan-bindiga su ka yiwa makarantar Firamare da ake kira LEA Primary School Kuriga 1 Kawanya, inda su ka kora daliban makarantar 'yan tsakanin shekaru 7 zuwa 15 da daya daga cikin malaman makarantar zuwa daji.
Malam Aminu Jibrin Gwadabe Kuriga haifaffen garin Kuriga ne kuma ya yi wa Muryar Amurka karin bayanin bayan da ya tabbatar da aukuwar lamari da ya faru.
Tuni dai rundunar ‘yan-sandan jihar Kaduna ta tura jami'an tsaro yankin don bin 'yan-bindigan cikin daji, inji mai magana da yawun rundunar, ASP Mansur Ibrahim.
Wannan dai ba shine karon farko da 'yan-bindiga ke sace dalibai a makarantun jihar Kaduna ba, abun da ya sa masana harkokin tsaro irin su Dr. Yahuza Ahmed Getso ke ganin akwai barazana a bangaren tsaro.
Idan dai hukumomi su ka tabbatar da cewa adadin daliban da aka sace sun kai 200 kamar yadda al’ummar yankin ke cewa, to daliban za su zama mafi yawa da kuma kankantar shekaru da aka taba sacewa a jihar Kaduna, abun da ke kara saka fargaba a zukatan dalibai da iyaye akan makomar makarantun jihar dake yankunan karkara.
Saurari cikakken rahoto daga Isah Lawal Ikara:
Dandalin Mu Tattauna