Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Koli Ta Tabbatar Da Zaben Uba Sani Da Nasir Idris Da Dapo Abiodun Da Sheriff Oborevwori


Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani
Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani

Kotun koli ta yi watsi da karar da dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Isah Ashiru ya shigar na kalubalantar nasarar gwamna Uba Sani na jihar Kaduna a zaben shekarar 2023.

Kotun kolin ta kuma tabbatar da hukuncin da kananan kotuna suka yanke wato kotun sauraron kararrakin zabe da kuma kotun daukaka kara, wadanda suka tabbatar da nasarar Uba Sani a zaben gwamna da aka gudanar a watan Maris na shekarar 2023.

Hukuncin dai ya kasance na bai ɗaya daga tawagar alkalan kotunn kuma ba a ci tarar kowa ba.

Idan ana iya tunawa, gwamna Uba Sani ya sami kuri'u dubu 730 da 2, inda ya doke abokin hamayyarsa Mohammed Ashiru na jam'iyyar PDP mai kuri'u dubu 719 da 196.

Kotun Koli Ta Kori Karar PDP Tare Da Tabbatar Da Nasarar Gwamna Nasir Idris Na Jihar Kebbi

Gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris
Gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris

Kotun kolin dai ta yi watsi da karar da Manjo Janar Aminu Bande mai ritaya na jam’iyyar PDP ya shigar na kalubalantar nasarar zaben gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi.

A hukuncin da ta yanke a yau Juma’a 19 ga watan shekarar 2024, tawagar alkalan kotun sun yi ittifaki kan cewa karar da dan takarar jam’iyyar PDP ya shigar ba ta da inganci kuma ba wanda aka ci tarar sa.

Idan ana iya tunawa, hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya wato INEC, ta bayyana Nasir Idris a matsayin wanda ya lashe zaben na jihar Kebbi da kuri’u dubu 409 da 225 inda ya doke abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP, Manjo Janar Aminu Bande mai ritaya wanda ya sami kuri'u dubu 360 da 940.

An sami ratar kuri’u dubu 48 da 285 tsakanin gwamna Nasir Idris da abokin hamayyarsa Manjo Janar Aminu Bande mai ritaya.

Kotun Koli Ta Kori Karar Adebutu, Ta Tabbatar Da Nasarar Gwamna Abiodun Na Ogun

Gwamnan jihar Ogun Dapo Abiodun
Gwamnan jihar Ogun Dapo Abiodun

Kotun kolin Najeriya ta yi watsi da karar da Ladi Adebutu na jam’iyyar PDP ya shigar na kalubalantar nasarar gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun a yau Juma’ah.

Karar kalubalantar nasarar Dapo Abiodun da Adebutu yi ya nuna cewa an sabawa dokokin zabe a zaben gwamna Abiodun kuma bai sami kuri’u mafi rinjaye ba don haka ya bukaci kotun ta soke zaben na ranar 18 ga watan Maris na shekarar 2023.

Sai dai a yau Juma’a, kotun kolin ta yi watsi da daukaka karar Adebutu a bisa rashin cancanta sannan ta tabbatar da nasarar Gwamna Abiodun a zaben na shekarar 2023.

Hukuncin dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da kotun koli ta jingine yanke hukunci kan zaben gwamnan jihar Ogun.

Idan Ana iya tunawa, kotunan sauraron kararrakin zabe da na daukaka kara sun yi watsi da karar na dan takarar jam’iyyar PDP a baya.

Gwamna Dapo Abiodun ya sami nasara a zaben gwamnan jihar Ogun ne da kuri’u dubu 276 da 298 inda ya doke abokan hamayyarsa da suka hada da Adebutu wanda ya sami kuri’u dubu 262 da 383 da kuma Biyi Otegbeye na jam’iyyar ADC wanda ya sami kuri’u dubu 94 da 754.

Kotun Koli Ta Tabbatar Da Zaben Oborevwori A Matsayin Gwamnan Jihar Delta

Gwamnar Delta Sheriff Oborevwori
Gwamnar Delta Sheriff Oborevwori

Hakazalika, A yau Juma’a ne kotun kolin Najeriya ta yi watsi da kararraki uku na neman a soke zaben Sheriff Oborevwori a matsayin gwamnan jihar Delta.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya wato INEC dai ta bayyana Sheriff Oborevwori na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna da aka gudanar a jihar Delta a ranar 18 ga watan Maris na shekarar 2023.

Sai dai sauran ‘yan takarar 3 bayan zaben ba su gamsu da sakamakon da hukumar INEC ta gabatar ba inda suka garzaya zuwa kananan kotuna biyu.

A yayin da Oborevwori ya yi nasara a kotun sauraron kararrakin zabe da kuma kotun daukaka kara, bangarorin 3 basu gamsu ba inda suka dauki matakin gaba na kalubalantar hukuncin kananan kotunan a Kotun Koli wanda ta zartar da hukuncinta a yau Juma’a 19 ga watan Janairun shekarar 2024 da muka shiga.

A lokacin da shari’ar ta jihar Delta ta taso a kotun koli a yau, kotun ta amince da hukuncin da aka yanke a baya tare da tabbatar da nasarar Oborevwori a matsayin zababben gwamnan jihar Delta.

A yayin zartar da hukuncinta kotun kolin dai ta fara ne da yin watsi da karar Sanata Ovie Omo-Agege na jam’iyyar APC da ya nemi a soke zaben Gwamna Oborevwori a bisa rashin iya tabbatar da zargin kada kuri’a fiye da kima da kuma rashin bin dokokin zabe.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG