Attajirin dan kasuwa, Aliko Dangote, ya kwato matsayinsa na attajirin da ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka, kamar yadda mujallar Forbes ta bayyana.
Matsayin, wanda kusan kullum mujallar Forbes ke bincike a kai da kuma sabuntawa game da yawam arziki da martabar kowane mutum da aka tabbatar ya zama hamshakin attajirin, ya nuna cewa dukiyar Dangote ta inganta da dala miliyan 10 inda a yanzu ya kai dala biliyan 10.1 daga 8 ga watan Janairun shekarar 2024 da muka shiga kwanaki 10 da suka gabata.
Dangote ya sha gaban Johann Rupert, hamshakin dan kasuwa mai sarrafa kayan alfarma na Afirka ta Kudu da danginsa.
Rahoton mujallar Forbes din ya yi nuni da cewa arzikin Rupert ya kasance dala biliyan 10, wanda ya ragu daga dala biliyan 10.7.
A yanzu dai, Aliko Dangote, wanda shi ne shugaban rukunin kamfanin Dangote, ya kasance a matsayi na 191 mafi arziki a duniya, a yayin da Rupert da iyalansa ke matsayi na 197.
Hakazalika, alkaluman rahoton Bloomberg ya kuma bayyana Dangote a matsayin wanda ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka.
A cewar Bloomberg, akasarin dukiyar Dangote ta samo asali ne daga hannun jarinsa na kaso 86 cikin 100 na simintin Dangote da ake sayarwa ga al’umma.
Dangote na rike da hannun jari a kamfanin kai tsaye kuma ta hannun kamfaninsa na rukunin kamfanin Dangote wato Dangote Industries.
Rahoton Bloomberg ya kara da nuna cewa, sauran kadarorin da Dangote ya mallaka a bainar jama’a sun hada da hannun jarin Sikarin Dangote, kamfanin NASCON Allied, da bankin UBA.
Hannun jarinsa a kamfanonin da ake hada-hada da jama’a ana gudanar da su ne kai tsaye kuma ta hannun rukunin kamfanonin Dangote, wadanda kuma ke gudanar da sana’o’in sarrafa abinci, taki, mai, da wasu masana’antu, in ji Bloomberg.
A cewar Bloomberg, dukiyarsa mafi daraja ita ce masana’antar sarrafa taki mai karfin samar da ton miliyan 2.8 na urea a duk shekara.
Ƙimanta dukiyar Dangote ta dogara ne akan tsarin kimanta arziki na kamfanin KPMG wanda manazarta daga wajen Bloomberg suka sake tabbatarwa.
Adadin kuɗaɗen Dangote sun dogara ne akan nazarin rabon riba na haraji, ma’amalolin cinikayyan cikin rukunin kamfanoninsa, da sauran abubuwan zuba kuɗi a ciki kamar jari.
Dandalin Mu Tattauna