Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sha Gaban Dangote A Matsayin Mutumin Da Ya Fi Kowa Arziki A Nahiyar Afirka


Aliko Dangote
Aliko Dangote

Hamshakin dan kasuwa, dan asalin kasar Afrika ta Kudu, Johann Rupert ya sha gaban attajirin dan kasuwa Aliko Dangote inda ya zama wanda ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka, kamar yadda mujallar Forbes ta fitar.

Haka zalika, hamshakan attajiran Najeriya Rabiu Abdulsamad mai kamfanin BUA da takwaransa Mike Adenuga mai kamfanin sadarwa na GLO sun rasa gurabensu a jerin hamshakan attajiran da mujallar kudin ta fitar.

A cikin jerin, dandalin hamshakan attajiran nan na Forbes Daily, wanda ke bin diddigin sauye-sauye na yau da kullun ga masu hannu da shuni a duk fadin duniya, ya bayyana cewa Aliko Dangote ya koma matsayi na biyu ne a yayin da dukiyarsa ta ragu daga dala biliyan 13 da miliyan 500 a shekarar 2023 zuwa dala biliyan 9 da miliyan 500 a farkon shekarar 2024 da muka shiga.

Wani binciken mujallar Forbes ya nuna raguwar arziki mai yawa a cikin attajiran sossai.

Haka kuma, arzikin attajirin dan Najeriya, Mike Adenuga, ya kai shi matsayi na goma a cikin jerin sunayen attajiran masu arzikin na nahiyar Afrika, a yayin da Patrice Motsepe, wanda ke matsayi na goma a shekarar 2023, ya rasa matsayinsa na goma mafi arziki a shekarar 2024.

Wani sauyi mai ban mamaki a cikin jerin masu arziki na Forbes a Afirka shi ne, babu wata mace da ta sami shiga jerin sunayen goma mafi arziki a farkon shekarar nan.

Masana tattalin arziki dai na alakanta raguwar arzikin wadannan attajiran da kalubalen da tattalin arziki a fadin nahiyar ke fuskanta.

Wasu kuma na danganta raguwar arzikin attajiri Dangote da faduwar darajar Naira da sauran batutuwan da suka shafi matsin tattalin arziki.

Ga jerin sunayen mafiya arziki a nahiyar Afirka da adadin kudinsu daga mujallar Forbes:

  1. Johann Rupert - Dala biliyan 10.3
  2. Aliko Dangote - Dala Biliyan 9.5
  3. Nicky Oppenheimer - Dala Biliyan 8.3
  4. Nassef Sawiris - Dala biliyan 7.4
  5. Abdulsamad Rabiu - Dala Biliyan 5.9
  6. Nathan Kirsh - Dala biliyan 5.8
  7. Issad Rebrab - Dala Biliyan 4.6
  8. Mohamed Mansour - Dala Biliyan 3.6
  9. Naguib Sawiris - Dala biliyan 3.3
  10. Mike Adenuga - Dala Biliyan 3.1

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG