Kamfanin rukunin Dangote a karon farko ya fito ya yi magana kan samamen da jami’an hukumar EFCC suka kai a hedkwatarsa da ke Legas a makon da ya gabata.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, kamfanin na Dangote ya ce a shirye yake ya ba hukumar ta EFCC hadin kai a bincike da take yi.
Jami’an EFCC sun kai samame hedkwatar kamfanin na Dangote a binciken da suke yi kan tarihin hadahadar kudaden waje da kamfanin ya yi da babban bankin Najeriya na CBN.
Hukumar ta EFCC a cewar kamfanin na Dangote ta turo masa da wasika tana bukatar bayanai kan yadda kamfanin ya yi hadahadar canjin kudaden kasashen waje tun daga 2014 zuwa wannan shekara.
Sanarwar ta kara da cewa ba kamfanin Dangote kadai aka turawa wannan wasika ba, hasali ma kamfanoni 51 aka turawa a Najeriya.
Ya kara da cewa kamfanin ya nemi hukumar ta EFCC da ta yi masa karin bayani da ba shi karin lokaci domin tattara bayanan duba da cewa na shekaru goma ake bukata.
Kamfanin na Dangote ya kara da cewa har ya turawa EFCC wasu bayanai a mataki na farko, amma jami’an hukumar suka ki karbar bayanan suka kuma matsa cewa sai sun kai ziyara hedkwatar kamfanin.
Wannan mataki a cewar rukunin kamfanin na Dangote ya zubar masa da kima.
Sai dai sanarwar ta kara da cewa akwai bukatar jama’a su fahimci cewa ba a samu wani rukunin kamfanin na Dangote da wani laifi ba, kuma a shirye yake ya taimakaw hukumar ta EFCC a bincike da take yi.
Dandalin Mu Tattauna