Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Kalubalantar Hukumomin Najeriya Kan Fasinjojin Da Aka Sace A Harin Jirgin Kasa Na Abuja Zuwa Kaduna


Fasinja a tashar jirgin kasa da ke Rigasa a Kaduna
Fasinja a tashar jirgin kasa da ke Rigasa a Kaduna

Ita dai gwamnati ta ce tana iya bakin kokarin wajen ganin ta kubutar da mutanen.

Shugabannin al’umma da na addini a Najeriya na kara nuna bukatar gwamnati ta matsa kaimi wajen ceto fasinjojin da a ka sace a sanadiyyar hari kan jirgin kasa a kan hanyar Kaduna a karshen watan Maris.

Kiran na zuwa ne wata daya da kimanin mako biyu da hari kan jirgin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan goma.

Masu kiran na nuna bukatar amfani da duk dabarun da su ka dace don karbo mutanen da lafiyar su da sada su da iyalan su.

Alkali a kotun sasanci ta jihar Katsina Barista Ibrahim Sabi’u Jibiya ya ce akwai bukatar ‘yan majalisar dattawa su sake nazartar dokar haramta biyan kudin fansa don ceto wadanda a ka sace, da nuna hakan na da hatsari ga rayuwar wadanda ke hannun miyagun irin a halin yanzu.

Muhammad Goma shugaban matasa ne na kungiyar makiyaya ta GAM Allah, yayin wata ziyarar da ya kai ofishin Muryar Amurka da ke Abuja, Najeriya ya koka kan yadda wasu ke yi wa dukkan makiyaya ko mazauna daji kudin goro ga aikata miyagun ayyuka.

Ita dai gwamnati ta ce tana iya bakin kokarin wajen ganin ta kubutar da mutanen.

Kusan duk masu niyyar takarar shugabancin Najeriya a 2023 na ambata magance kalubalen tsaro a matsayin babbar ajandarsu in sun haye karaga.

Saurari cikakken rahoton Saleh Shehu Ashaka:

Ana Ci Gaba Da Kalubalantar Hukumomin Najeriya Kan Fasinjojin Da Aka Sace A Harin Jirgin Abuja Zuwa Kaduna - 2'56"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

Kudurin wasu 'yan Najeriya na sabuwar shekara a fannin lafiya, da wasu sauye-sauyen da suke fatan yi don samun nasara a rayuwarsu
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 1080p

No media source currently available

0:00 5:16 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 1080p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Karo na biyu kenan a Nijar ake gudanar da bukukuwan Kirsimetin karkashin mulkin soja, inda a bara takunkumin ECOWAS ya dakushe farin cikin
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:52 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG