Na kan dauki wata matsala ko wani abun da ake yayi a cikin al’umma domin yin fim da shi tare da nusar da al’umma abinda wannan dabi’a kokuma abinda ake yayi ke nufi inji furudosa Salim Muktar Maidu, wanda aka fi sani da Dan Hisbah.
Ya ce misali a fim dinsa na Ibro dan Hisba a wancan lokaci ya nuna ayyukan da hukumar Hisbah ke nufi ga al’umma ganin cewar a wancan lokaci mutane sunyi wa ayyukan hukumar mummunar fimta, inda fim din ya nuna ayyukansu da muka tasirinsu a cikin al’umma.
Dan-hisbah ya kara da cewa haka a yanzu ya dauki dabi’ar nan ta ‘yan bangar siyasa tare da nuna dalilan da ke jefa matasa cikin bangar siyasa da ma makomarsu, me ke hassasa matashi ya koma dan jagaliya, inda yayi wa fim din lakabi da “A rabu da maza”
Dan-hisbah ya ce da dama yana ganin canji a wasu al'ammura ta hanyar fadakar da mutane ko isar da wani sako domin al’umma su fuskanci me wannan abu ke nufi.
Facebook Forum