Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gurbattaccen Yanayi Na Sanadiyar Rayukan Yara Milliyan 1.7, 'Yan Kasa Da Shekaru 5


Gurbatar yanayi na haddasa matsaloli da dama, ana iya cewa yaro daya cikin hudu ke ‘yan kasa da shekaru 5, ke mutuwa a fadin duniya, wanda adadin su ya kai milliyan daya da dubu dari bakwai.

Hukumar kiwon lafiya ta duniya, ta tabbatar da cewar idan har ba’a dauki kwararan matakan kawo karshen gurbatar yanayi ba, mutuwar zata karu matuka,

Hukumar ta gwada matsalolin da gurbatar yanayi kan haifarwa ga yara, da fitar da hanyoyi biyu don magance hakan, a wani bincike da suka gudanar, mai take “Riko da yanayi mai dorewa a duniya” da “Maida hankali ga lafiyar yara da yanayi.”

Burin shine kada a gurbata yanayi, don kariya ga yara da yanayin da jama’a ke rayuwa, domin samun lafiya mai inganci. A cewar masana, gurbattacciyar iska da jarirai ke shaka, na zama sanadiyyar mutuwar yara sama da milliyan 6.5 a kowace shekara.

Lamarin ya hada da yara sama da 600,000 masu shekaru daga daya zuwa biyar da haihuwar. Margaret Chan, darakta janaral ta hukumar kiwon lafiya ta duniya, ta bayyana cewar kananan yara suna cikin hatsari na mutuwa a lokacin da suke da kananan shekaru.

Mafi akasarin yaran dake mutuwa sanadiyar gurbataccen yanayi sun fito daga kasashe masu tasowa ne, wanda gurbatacciyar iska da ake shaka keda alaka da kasashe masu arziki da masu fama da talauci.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG