WASHINGTON D.C —
Masu binciken kimiyya a Afirka ta kudu sun fitar a bainar jama'a wani kwarangwal na kakannin bil’adama da aka samu mai sama da shekaru Miliyan daya da dubu dari biyar a duniya.
A jiya Laraba ne Jami’ar Witwatersrand, ta nuna kwarangwal din wanda ke da kusan duk cikakkun kasusuwan sa.
Ana kyautata zaton Kwarangwal din nada kusan shekaru Miliyan Uku da dubu dari shida, kuma zai taimakawa masu binciken kimiyya fahimtar kamanni da yanayi da yadda kakannin bil’adama ke tafiya da sauransu.
Masana sun bayyana cewa an kwashe tsawon shekaru ashirin wajan ginowa, da gogewa da kuma harhada kasusuwan tsohon kwarangwal din.
Facebook Forum