Kwanaki kadan da suka gabata gwamnatocin Najeriya da Nijer suka dawo da daruruwan matasa da suka sami kawunan su cikin mawuyacin hali a kasar Libya, wane mataki ya kamata gwamnatoci su dauka akan wadannan matasa da aka mayar ksashen su?
Hukumomi sun dade suna jan kunne da wayar da kai ga matasa maza da mata akan hatsarin dake tattare da ketarawa wasu kasashe ta barauniyar hanya, kuma rahotanni sun bayyana yadda ake sayar da wasu da dama a matsayin bayi a kasar Libya, amma har yanzu lamarin yaki ci yaki cinyewa, ina shawara?
Muna bukatar sakonnin maza da mata akan wannan tambaya, kuma za’a iya aiko mana da sakon ta murya a kafar sada zumunta ta WhatsApp mai lamba +12025775834. Kada a manta a fadi suna da kuma jiha ko gari.
Ana iya sauraren wannan shiri a duk lokacin da ake bukata a shafinmu mai adireshi www.dandalinvoa.com
Facebook Forum